Za a kafa kwamiti mai ƙarfi don gudanar da bincike kan gobarar da ta tashi a Makarantar Alƙur'ani da Larabci ta Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi.
Gwamnan jihar, Nasir Idris, ya bayar da umarnin a ƙarshen mako.
Gobarar ta faru ne a ranar Asabar da yamma, wadda ta lalata ɗakunan kwanan dalibai da azuzuwa da dama, ta kuma haifar da rudani tsakanin ɗalibai da mazauna.
Gwamnan jihar, wanda ke kan hanyarsa ta yin buda baki a watan Ramadan, ya lura da hayaki mai kauri a gefen hanya, sannan ya umurci ayarin motocinsa da su tsaya, bayan ya gano cewa hayakin yana fitowa daga makarantar, ya ba da umarnin a kwashe ɗalibai nan take, sannan ya sanar da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi da sauran masu ba da agajin gaggawa don tabbatar da an shawo kan lamarin.
Shiga tsakani da gwamna Nasir Idris ya sa aka kai ga wuraren da lamarin ya faru ba tare da ɓata lokaci ba, wanda gwamnan duk da yin azumin, ya zauna a wurin na tsawon awanni, yana kula da kwashe ɗalibai sama da 140 tare da tabbatar da an gano inda suke.
Na tsawon kimanin awanni uku zuwa huɗu, masu kashe gobara sun yi ta fama da gobarar kafin su shawo kan lamarin.
A cewar gwamnan, "Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da cewa babu wani rai da aka rasa a wannan lamari. Tsaron 'ya'yanmu ya kasance babban abin da wannan gwamnati ke bukata. Ba za mu yi wa wannan lamari wasa ba."
Ya yaba da kokarin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi saboda gaggawa da kuma matakin da suka dauka na kwarewa, yana mai cewa kokarinsu ya hana abin da ka iya zama babban bala'i.
Ya tabbatar wa iyaye da masu kula da su cewa dukkan daliban suna cikin koshin lafiya kuma an mayar da su wani lokaci zuwa babban reshen makarantar har sai an sake tantance gine-ginen da suka lalace.
A cikin makonni masu zuwa, ana sa ran kwamitin bincike zai gabatar da rahotonsa.
