An tabbatar da Arsenal za ta lashe gasar Premier ta kakar wasa ta 2025/2026.
Wannan ya biyo bayan kunnen doki da Manchester City ta yi da Bournemouth a daren Talata.
'Yan wasan Pep Guardiola sun bukaci su doke Cherries domin ci gaba da fafatawa a gasar har zuwa ranar karshe.
Amma wannan sakamakon yana nufin ba za su iya kama Arsenal da wasa daya ba.
Kroupi Junior ne ya fara zura kwallo a ragar Bournemouth da bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya yi wa Gianluigi Donnarumma.
City ta yi fama wajen sauya 'yan damar da ta samu.
David Brooks ya rasa damarmaki biyu don ninka yawan kwallayen da masu masaukin baki suka ci, kafin Erling Haaland ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Yanzu za a bai wa Arsenal kofin a wasan ranar Lahadi a Crystal Palace.
