Ƙungiyar LaLiga ta yanke shawarar ne kasa da sa'o'i 24 bayan ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 3-2 a wasan ƙarshe na SuperCopa.
Bayan wasan, Alonso ya fito ya ce ita ce gasar "mafi ƙarancin muhimmanci" da za su buga.
"Real Madrid CF ta sanar da cewa, bisa yarjejeniyar da ta yi tsakanin ƙungiyar da Xabi Alonso, an yanke shawarar kawo ƙarshen lokacinsa a matsayin kocin ƙungiyar farko," in ji sanarwar da ƙungiyar ta fitar.
"Xabi Alonso zai kasance koyaushe yana da ƙauna da sha'awa daga dukkan magoya bayan Madrid saboda shi gwarzo ne na Real Madrid kuma koyaushe yana wakiltar ƙimar ƙungiyarmu. Real Madrid za ta kasance gidansa koyaushe.
"Ƙungiyarmu tana godiya ga Xabi Alonso da dukkan ƙungiyar fasaha saboda aikinsu da jajircewarsu a wannan lokacin, kuma muna yi musu fatan alheri a wannan sabon matakin rayuwarsu."
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Spain ya daɗe yana fuskantar matsin lamba, yayin da ƙungiyar ke ci gaba da fama a gasar LaLiga da kuma gasar zakarun Turai.
Shawarar da Madrid ta yanke na raba gari da Alonso, ta zo ne kwana biyu kafin wasansu na gaba - zagaye na 16 a gasar Copa del Rey da Albacete.
